An dai gudanar da wani buki don tunawa da wadanda suka rasu a harin.
Daya daga cikin malaman makarantar da aka kai harin Andaleeb Aftab wacce ta rasa danta ta bayyana lokacin da ta ga 'yan makaranta na guje guje lokacin da harin:
Rahotanni sun ce daukacin makarantu a lardin Khyber Pakhtunkhwa sun bude bayan karin hutun da suka yi saboda harin.
A 'yan watannin nan gwamnatin Pakistan ta dawo da zartar da hukuncin kisa a kasar, yayin da ake yunkurin kafa kotunan soji don gurfanar da masu aikata laifuffukan ta'adanci.ABNA